Home Labaru El-Rufai Ga Tinubu: Ka Sallami Duk Wanda Ya Gaza Kokari A Gwamnatin...

El-Rufai Ga Tinubu: Ka Sallami Duk Wanda Ya Gaza Kokari A Gwamnatin Ka

25
0
Tinubu El Rufai
Tinubu El Rufai

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shawarci shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kori duk wanda ya gaza aiki tukuru a gwamnatin sa.

Nasir El-Rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri a ranar Litinin, inda ya yi kira ga shugaban kasan ya kuma yi la’akari da muradin cimma yiwuwar wasu manufofin gwmnatin.

Ya ce idan an ba mutum matsayi kuma ba ya aiki kamar yadda aka yi tsammani, ya kamata a tsige shi.

El-Rufai ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya su yi addu’o’i sannan su mara wa gwamnati mai ci baya domin daidaitawar al’amura a kasa.

Leave a Reply