Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriya na ci gaba da biyan tallafin mai wani abu da ya ce ‘yan Najeriya da dama ba su sani ba.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, El Rufai ya ce a yanzu gwamnati na biyan fiye da abin da take biya a matsayin tallafin mai a baya.
Ya bayyana cewa matakai da dama da aka tanada na rage raɗaɗin janye tallafin mai ba su tasiri abin da a cewar sa ya sa aka maido da tsarin biyan tallafin.
El Rufai ya ce wurin aiwatar da tsarin, kamar yadda ake gani, gwamnatin a yanzu ta gano cewa dole a ci gaba da biyan tallafin, kuma tana biyan kuɗi mai yawa kan tallafi fiye da yadda take biya a baya, ya ce tsare-tsaren da aka shirya domin rage tasirin cire tallafin ba su yi wani tasiri ba, don haka gwamnatin tarayya ta koma biyan tallafin man.
Ya ce mutane da dama ba su san cewa gwamnati tana ci gaba da biyan tallafin mai ba, amma idan suna son su san ko ana biya ko a a, su duba farashin mai da dizel saboda kamata ya yi Fetur ya fi tsada a kan dizel amma farashin dizel ya haura naira dubu ɗaya yayin da man fetur yake kan naira 600 duk lita guda.