Home Labaru Yawan Marasa Aiki a Nijeriya Zai Karu Zuwa Kashi 41 a 2023

Yawan Marasa Aiki a Nijeriya Zai Karu Zuwa Kashi 41 a 2023

134
0

Kamfanin ba da shawara a kan haraji na duniya KPMG, ya yi
hasashen cewa rashin aikin yi a Nijeriya zai karu zuwa sama
da kashi 40 da rabi cikin 100 idan aka kwatanta shi da na
shekara ta 2022 na kasha 37 da rabi cikin 100.

KPMG ya yi cikakken bayanin hasashen ne a cikin rahoton Hasashen Harkokin Tattalin Arziki na Duniya, inda ya ce ana sa ran rashin aikin yi zai cigaba da zama babban kalubale a shekara ta 2023, saboda karancin jarin da kamfanoni masu zaman kan su ke fuskanta.

Kwamitin ya kara da cewa, karancin masana’antu sannu a hankali zai kara tabarbare tattalin arziki.

Rahoton, ya ce ana sa ran za a samu koma-bayan tattalin arzikin duniya a shekara ta 2023, da kuma tasirin sa na ciniki da hada-hadar kudi, lamarin da zai haifar da mummunan tasiri ga manufar sake fasalin Naira da aka gabatar a karshen shekara ta 2022 da farkon shekara ta 2023.

Leave a Reply