Hukumar ƙwallon kafa ta duniya, Fifa ta bai wa Saudi Arabia damar gudanar da gasar cin kofin duniya a 2034 a babban taron da ta yi ranar Laraba.
Haka kuma hukumar ta tabbatar da cewar Sifaniya da Portugal da Morocco za su shirya wasannin da za a yi a 2030 a babbar gasar tamaula ta duniya.
Gasar kofin duniya da za a yi a 2030 za a yi wasu wasannin a Argentina da Paraguay da Uruguay, domin bikin shekara 100 da fara gasar.
An amince da wannan hukuncin bayan kaɗa kuri’a da aka gudanar a babbar taron hukumar ƙwallon kafa ta duniya da ta yi ranar Laraba.