Home Labarai Garba Shehu:  Buhari Ya Kasance Shugaba Mai Gaskiya da Tausayin Talaka

Garba Shehu:  Buhari Ya Kasance Shugaba Mai Gaskiya da Tausayin Talaka

71
0
OIP (3)
OIP (3)

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kasance mutum mai gaskiya da amana da tausayin talakawa.

Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, a ranar da tsohon shugaban yake murnar cika shekara 82 a rayuwarsa.

Garba Shehu ya ce, “Buhari shugaba ne daban, wanda yake damuwa da damuwar talakawa da masu rauni, sannan yake dagewa wajen inganta rayuwar talakawa da fitar da su daga cikin ƙunci.”

Garba Shehu ya ce siyasa da cin hanci da rashawa ɗanjuma ne da ɗanjumai a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya. “Tunanin mutane shi ne duk ɗansiyasa ɗan rashawa ne. Amma shi sunansa “Mai gaskiya” saboda gaskiyarsa da rashin ɗaukar duniya da zafi.

Garba Shehu ya ƙara da cewa Buhari ya yi kamfe ne kan inganta tattalin arziki da samar da tsaro da yaƙi da rashawa.

A zamanin mulkinsa, ƙasar ta ga yadda aka ɗauki matakai masu yawa domin yaƙi da talauci. Buhari ya mayar da hankali kan inganta kiwon lafiya, inda a zamaninsa aka cire ƙasar daga cikin masu fama da cutar polio.

Leave a Reply