’Yan kasuwa sun bayyana ƙwarin gwiwar cewa farashin man fetur zai ragu a Nijeriya sakamakon fara lodin tataccen mai daga Matatar Fatakwal.
Hakan na zuwa ne a yayin da ’yan kasuwa suka yi marhabin da fara fitar da tataccen mai daga matatar mai ta Fatakwal, inda suke sa ran hakan zai kawo gasa da inganci da kuma faɗuwar farashin man.
Sun ce bayan watanni 11 matatar man ta fara lodin kayayyakin man fetur, inda a halin yanzu motoci kusan 100 ke lodin mai daga matatar zuwa sassan Nijeriya.
Kamfanin NNPC ya sanar da fara fitar albarkatun man fetur daban-daban da suka hada da man fetur, dizal, da kalanzir daga matatar Fatakwal a ranar Talata.
Shugaban Kamfanin na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara ga Nijeriya, wanda ke nuna sabon zamani na ’yancin kai a fannin makamashi da bunkasar tattalin arziki.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya gaggauta farfaɗo da matatar man ta Kaduna da Warri da sauran su,
domin bunƙasa samar da mai a cikin gida da kuma mayar da Najeriya babbar cibiyar makamashi.