Home Labaru Mutum 17 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Garkuwa Da Mutane a Ekiti

Mutum 17 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Garkuwa Da Mutane a Ekiti

68
0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti, ta gurfanar da wasu mutane
17 da ake zargi da aikata laifuffuka tare da kwato wasu
makamai a hannun su.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ogundare Dare, ya ce rundunar ta kama mutanen da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban.

Da ta ke gabatar da wadanda ake zargin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP Sunday Abutu, ta ce jami’an su sun kama wani Augustine Agboobo da Adeniyi Olamilekan da Williams Ukeuima Friday da Ademoh Gabriel a cikin dajin da ke kusa da yankin gonakin Igede.

Yayin da ake yi masu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa su ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane ne, wadanda su ka gudanar da ayyukan garkuwa da mutane a jihar Ekiti ciki har da sace Ajibade Adeleke a gonar Igede tare da karbar kudin fansa.

Abutu ta kara da cewa, rundunar ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, tare da hadin gwiwar wasu al’umma a Oke-Ureje da ke Ado-Ekiti.

Leave a Reply