Home Labarai Yaki Da Almundahana: Manyan Ɓarayi Ma Ba Za Su Tsira Ba A Hannunmu...

Yaki Da Almundahana: Manyan Ɓarayi Ma Ba Za Su Tsira Ba A Hannunmu – EFCC

48
0

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC
Mista Ola Olukoyede ya tabbatar da cewa ba zai bar manyan
ɓarayi ba a yaƙin da suke yi da masu alaƙa da cin hanci da
rashawa,


Mista Ola Olukoyede ya ce ba za su bar kowa ba a aikin da suke yi. Ya ce a daidai lokacin da suke bin manyan ɓarayi, za kuma
su ci gaba da bin sawun ƙananan ɓarayi.


Shugaban na EFCC ya ba da wannan tabbaci ne a lokacin da hukumarsa ta shirya wani taron wayar da kai da kuma yunƙurin shigar da jama’a cikin harkokin yaƙi da cin hanci da rashawa.


A cewarsa, a cikin wata biyun da ya wuce, hukumarsa ta EFCC ta gurfanar da tsoffin gwamnoni guda biyu gaban shari’a. Ana dai sukar hukumar ta EFCC da cewa ta zama kyanwar lami, ba ta iya bin manyan ‘yan siyasa da sauran manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati waɗanda ake zargi da tafka gagarumar sata da kuma almundahana da dukiyar al’umma.


Sai dai, Mista Ola Olukoyede ya ce ba gaskiya ba ne a ce EFCC ta fi kauri wajen kama masu damfarar intanet.

Leave a Reply