Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Wata Sabuwa: An Bukaci Kotun Zabe Ta Dakatar Da Rantsar Da Shugaba Buhari

Jam’iyyar Hope Democratic Party HDP, ta shigar da wata kara da ke neman kotun sauraren kararrakin zaben Shugaban kasa ta bada umurnin dakatar da rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu.

Haka kuma, Jam’iyyar ta bukaci a hana rantsar da Shugaban alkalan Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

A wani jawabi da manema labarai suka samu a ranar Talata, 14 ga watan Mayu, ta shigar da kara akan dalilai shida daidai da sashi daya ayan na biyu a kundin tsarin mulkin 1999.

Wasu daga cikin dalilan jam’iyyar na shigar da karar su ne, cewa akwai wata shari’a a kasa da ke kalubalantar nasarar shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shekara ta 2019. Jam’iyyar ta kara da cewa, duk da shari’ar da ake yi da Shugaba Muhammadu Buhari, amma ana ta kokari da shirye-shiryen rantsar da shi da Shugaban alkalan Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu.

Exit mobile version