Jami’an Ofishin Babban Kwamishinan Kula da ‘yan gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya, sun ce masu gudun hijira sama da 90,000 da su ka tsere daga Nijeriya zuwa yankin Kamaru su na nan kalau kuma ana kokarin dawo da su gida.
Mutanen da su ka yi hijirar dai akasarin su daga jihar Borno su ke, kuma sun yi kaura ne saboda hare-haren da mayakan Boko Haram ke yawan kai masu.
Da ya ke jawabi a wajen wani taron manema labarai, kwamishinan Yada Labarai na jihar Adamawa Ahmed Sajoh, ya ce ana shirin kwaso mutanen daga sansanin Minawawo da ke cikin Maiduguri zuwa wani sansanin da za su fara yada zango a Jihar Adamawa.
Ya ce Kusan mutane 4,000 daga masu hijirar ‘yan Jihar Adamawa ne, don haka wasu kauyuka sun amince su karbi mutane 1,500 daga na jihar Borno, wadanda su ka nuna sun amince su zauna a jihar Adamawa.
Wakilin Jihar Borno a wajen taron Kulima Kachalla, ya gode wa zumuncin da Jihar Adamawa ta nuna, sannan ya ce jihar Borno za ta bada hadin kai wajen ganin aikin jigilar kwaso ‘yan gudun hijirar ya yi nasara.
You must log in to post a comment.