Home Labaru Ilimi Sabon Ministan Ilimi Ya Soke Ƙudurin Cika Shekara 18 Kafin Shiga Manya...

Sabon Ministan Ilimi Ya Soke Ƙudurin Cika Shekara 18 Kafin Shiga Manya Makarantu A Najeriya

58
0
Website post 9 jpg e1690919576672
Website post 9 jpg e1690919576672

Sabon ministan Ilimi, Olatunji Alausa, ya soke dokar da ta buƙaci sai ɗalibi ya kai shekara 18 kafin shiga jami’a wanda tsohon ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya kawo.

Olatunji Alausa ne ya bayyana wannan mataki a jawabin sa na shiga ofishi a matsayin sabon ministan Ilimi a ranar Talata.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya naɗa shi bayan cire tsohon ministan ilimi Tahir Mamman sakamakon sake fasalin ministocin sa.

sannan ya sauya wa ƙaramin ministan ilimi, Yusuf Sununu, ma’aikata zuwa ma’aikatar hukumar jin-ƙai da yaƙi da talauci.

A makon da ya gabata ne aka cire Tahir Mamman daga kujerar sa wanda kafin lokacin ya umarci hukumar tsara jarrabawar shiga jami’a ta ƙasa wat (JAMB) da kuma manyan makarantu a Najeriya kan ka da su ba wa kowanne ɗalibi da bai kai shekara 18 ba gurbin karatu.

Leave a Reply