Shugaba Bola Tinubu ya daga likkafar Babban Hafsan Sojin Kasa Nijeriya na riko, Olufemi Oluyede zuwa Laftanar Janar.
Kakakin fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar da karin girman a fadar shugaban kasa.
An daga likkafarsa ne kwanaki bayan da Shugaba Tinubu ya nada shi mukamin a mataki na riko.
A nasa bangaren, Laftanar Janar Oluyede ya bayyana matukar godiya tare da martaba lamarin.
Ya jaddada aniyar dabbaka muradan Laftanar Janar Taoreed Lagbaja tare da tabbatar da zaman lafiya a fadin Nijeriya.
Matukar Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi zai kasance cikakken babban hafsan sojin da zai maye gurbin Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a mataki na dindindin.