Home Labarai Kirkiro Masarautu: Fintiri Zai Samar Da Kartin Sarakuna A Jihar Adamawa

Kirkiro Masarautu: Fintiri Zai Samar Da Kartin Sarakuna A Jihar Adamawa

159
0
Screenshot 2022 11 26 at 7.30.47 PM 780x470
Screenshot 2022 11 26 at 7.30.47 PM 780x470

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da shirin gwamnatin sa na ƙirkiro da sabbin masarautun gargajiya bisa hujjar ƙarin buƙatar hakan daga ɓangarorin al’ummar jihar da dama.

Gwamna Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙabilar Heba daga ƙaramar hukumar Hong.

ya ce nan ba da jimawa ba zai aika da ƙudirin dokar ƙirkiro masarautun ga majalisar dokokin jihar domin ya zama doka.

Ya ci gaba da cewa yana so ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi nazari kan bukatar su dan ta amince ko akasin haka.

kuma idan aka gano akwai buƙatar a samar da masarautar Heba ba za a yi ƙasa a gwiwa ba wajen aika ƙudirin ga majalisar dokoki.

Leave a Reply