Home Labarai Kisan-Gilla: Mahara Sun Kashe Manoma 10 A Jihar Neja

Kisan-Gilla: Mahara Sun Kashe Manoma 10 A Jihar Neja

32
0
2ead028500334405
2ead028500334405

’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Wayam da Belu-Belu a Ƙaramar Hukumar Rafi da ke Jihar Neja, inda suka kashe aƙalla manoma 10, ciki har da mata, sannan suka sace wasu.

Harin ya faru ne da safiyar Talata lokacin da mutanen ƙauyen ke sallar Asuba.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa an sare kan mutum shida daga cikin waɗanda aka kasha, hakazalika sun ce maharan sun jikkata wasu da dama.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin Bala Tukur, ya ce ‘yan bindigan sun kashe mutum 10 babu tausayi, ya ce harin ya kawo cikas ga aikin noma a yankunan.

Inda wasu mazauna yankin aka tilasta musu biyan kuɗin haraji kafin shiga gonakin su don girbe amfanin gona.

’Yan bindigar sun kuma kai hari garin Zungeru inda suka sace mutane da dama, ciki har da Indiyawa biyu da ke aiki a gonar shinkafa a Borgu.

Gwamnatin Jihar Neja, ta sanar da cewa tana sane da lamarin, inda Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed ya ce, an tura jami’an tsaro domin su magance matsalar da kuma hana sake faruwar hakan a gaba.

Leave a Reply