Hukumomi da jama’a a jihar Sokoto na nuna damuwa kan ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ke gudanar da harkokin ta a wasu ƙananan hukumomin jihar biyar.
Mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ne ya bayyana haka a yayin gabatar da wata maƙala a lokacin da ɗaliban kwalejin horon soja (NDA ) da ke Abuja suka kai wa jihar ziyara a ranar Juma’a da ta gabata.
Mataimakin gwamnan ya shaida cewa ‘yan ƙungiyar da ake wa lakabi da Lakurawa, waɗanda suke ɗauke da manyan makamai, suna yawo tare da wa’azi ga mazauna yankunan ƙananan hukumomin Tangaza da Gudu da Illela da Binji da kuma Silame.
Wata majiya ta shaida cewa ‘yan ƙungiyar sun shiga yankunan na Sokoto ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.
Sukan yi wa’azi tare da cewa su ba su tare da ‘yansanda da sojoji, da ma duk wani jami’in gwamnati na siyasa kuma ba su yarda da karatun boko ba.