Allah Ya yi wa babban yayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, Alhaji Suleiman Sambo, rasuwa a ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya.
Marigayi Alhaji Suleiman Sambo, ya rasu yana da shekara 82 a duniya, kuma tuni aka yi jana’izar sa.
Cikin gajeriyar nasihar da ya gabatar yayin jana’izar, babban limamin masallacin kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, Uztaz Sadiq Yusuf, ya gargadi al’ummar Musulmi su mayar da hankali wajen bautar Allah.
Ya yi nuni da irin gudunmawar da marigayin ya bayar a lokacin da yake raye.
Marigayi Alhaji Suleiman Sambo, ya yi aiki a ma’aikatar buga takardu ta gwamnati ƙarƙashin tsohuwar ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna.
Ya yi ritaya a matsayin babban Sufeto a 1994 bayan kwashe shekaru 35 yana aikin gwamnati.