Home Labaru Harin Sama: Sojin Saman Nijeriya Sun Hallaka Manyan Dakarun Boko Haram Sama...

Harin Sama: Sojin Saman Nijeriya Sun Hallaka Manyan Dakarun Boko Haram Sama Da 30 A Borno

25
0
rjQjGXJ1 400x400
rjQjGXJ1 400x400

Rundunar sojojin saman Nijeriya, ta yi nasarar kashe manyan ‘yan ta’adda Ali Dawud, da Bakurah Fallujah, da Mallam Ari, da wasu 30 a Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Edward Gabkwet ya fitar, ya ce rundunar ta kai hari ne kan maboyar ‘yan ta’addar ISWAP da ke kauyen Kolleram a gabar tafkin Chadi.

A cewar sa, rundunar ta gudanar bincike a yankin inda ta gano ‘yan ta’adda tare da kashe sama da 30, kuma daga cikin wadanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandojin Boko Haram irin su Ali Dawud, Bakura Fallujah, da Mallam Ari.

Ya ce harin na sama ya kuma lalata wa ‘yan ta’addan motoci, da babura, da kuma makamai.

 Ya kara da cewa nasarar da sojojin suka samu ta nuna aiki tukuru da suke yi na son kawar da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiyar ‘yan Nijeriya.

Leave a Reply