Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya gargaɗi ‘yan Nijeriya su riƙa tauna magana kafin su furta ta, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar tsaro.
Buhari ya bayyana haka ne, a cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya fitar.
Shugaba Buhari, ya ce bai dace a ce waɗanda su ke kan madafun iko kuma shugabannin al’umma su na furta maganganu ba tare da tauna su ba.
Ya ce dole ne shugabanni su zo a haɗa kai wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro da ake fama da ita a Nijeriya ba a riƙa magana da son rai ba.
Da ya ke tsokaci a kan yadda ake alakanta matsalar tsaro da siyasa a Nijeriya, shugaba Buhari ya ce yin hakan ba abu ne da ya dace a ce ana yi ba.