Home Labaru Kungiyar ACF Za Ta Yi Raddi A Kan Wasikar Obasanjo

Kungiyar ACF Za Ta Yi Raddi A Kan Wasikar Obasanjo

345
0
Arewa Consultative Forum
Arewa Consultative Forum

Kungiyar Arewa Consultative Forum ta yi raddi  a kan wasikar da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari.

Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa
Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya

Kungiyar ta ce, har yanzu tana karanta wasikar kuma za su mayar da martani nan ba da dadewa ba, kamar yadda kakakin kungiyar,Muhammad Ibrahim Biu ya bayyana.

A bangare guda, kungiyar Miyetti Allah ta yi kira ga hukumomin tsaro su kama Olusegun Obasanjo kan wasikar da ya aikewa shugaba Buhari.

Karanta Wannan; Obasanjo Ya Sake Rubuta Wa Shugaba Buhari Wasika

Tsohon shugaban kasar dai, ya sake aikewa shugaba Muhammadu Buhari wasika, inda ya ke gargadin cewa, Nijeriya na cikin halin ha’ula’i, kuma shugaban kasa ne kadai ke iya ceto ta.

Ya ce tun lokacin da Buhari ya hau mulki, Nijeriya ta shiga cikin mumunan halin rashin tsaro, wanda ba a taba gani ba a tarihin Nijeriya.

Obasanjo ya yi kira ga makiyaya su fito su bayyana abubuwan da suke bukata, domin a samu zaman lafiya sabanin kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasar’nan.

Leave a Reply