Majalisar Dattawa ta ce za ta tantance shugaban Alkalan Nijeriya mai shari’a Ibrahim Tanko Mohammed, domin tabbatar da shi a matsayin mai cikaken iko a ranar Laraba 17 ga watan Yuli.
‘Yan Majalisar dai sun cimma wannan matsaya ne, bayan an jefa kuri’a a akan lamarin bisa jagorancin Shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan.

Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad zai fuskanci kwamitin tantancewa ne da ya kunshi dukkan ‘yan majalisar.
Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya mika wa majalisa sunan Ibrahim Tanko domin tantance shi a matsayin shugaban alkalai kamar yadda sashe na 23(1) da kudin tsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999 ya tanada. �
You must log in to post a comment.