Home Coronavirus Dokar Korona: An Fara Hana Ma’Aikata Shiga Ma’Aikatun Gwamnati A Jihar Edo

Dokar Korona: An Fara Hana Ma’Aikata Shiga Ma’Aikatun Gwamnati A Jihar Edo

10
0
Covid Card

Dokar hana shiga ofisoshin gwamnati ta sai an nuna katin shaidar riga-kafin korona ta fara aiki a Jihar Edo.

A ranar Larabar da ta gabata ne, aka hana kowa shiga Gidan Gwamnantin Jihar Edo sai wanda ya nuna katin shaidar riga-kafin korona.

Tun farko dai Gwamna Godwin Obaseki ya sha alwashin cewa, daga mako na biyu na watan Satumba dokar za ta fara aiki a fadin jihar sa.

Dokar kuwa ta haɗa da hana shiga masallatai da coci-coci sai da katin shaidar riga-kafin korona a jihar Edo.

Wata majiya ta ruwaito yadda aka jibge jami’an ‘yan sanda a ƙofar shiga Gidan Gwamnantin, inda su ke aikin hana ma’aikata shiga sai mai dauke da katin shaidar riga-kafin korona.