Home Labaru Harin Buhari: Bisa Kuskure Jirgin Yaki Ya Kashe Fararen Hula A Yobe...

Harin Buhari: Bisa Kuskure Jirgin Yaki Ya Kashe Fararen Hula A Yobe – Sojin Nijeriya

12
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya, ta ce a kan kuskure ne jirgin dakarun ta ya kai hari tare da kashe fararen hula a garin Buhari da ke karamar hukumar Yunusarin a jihar Yobe.

Shaidu sun ce, harin jirgin saman ya yi sanadin kashe aƙalla mutane goma, baya ga gommai da su ka jikkata ciki kuwa har da mata da ƙananan yara.

Da farko rundunar sojin ta musanta faruwar lamarin, amma daga bisani ta fitar da wata sanarwa ta na bayyana kuskuren da ya faru har aka samu wannan hatsari.

Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na rundunar sojin Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce jiragen sojin su na shawagi ne domin tattara bayanan sirri a kan ayyukan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Ya ce Rundunar Operation Hadin Kai ta samu bayanan cewa ana aikata ayyukan ta’addanci a kan iyakar Nijeriya da Nijar.