Dokar hana shiga ofisoshin gwamnati ta sai an nuna katin shaidar riga-kafin korona ta fara aiki a Jihar Edo.
A ranar Larabar da ta gabata ne, aka hana kowa shiga Gidan Gwamnantin Jihar Edo sai wanda ya nuna katin shaidar riga-kafin korona.
Tun farko dai Gwamna Godwin Obaseki ya sha alwashin cewa, daga mako na biyu na watan Satumba dokar za ta fara aiki a fadin jihar sa.
Dokar kuwa ta haɗa da hana shiga masallatai da coci-coci sai da katin shaidar riga-kafin korona a jihar Edo.
Wata majiya ta ruwaito yadda aka jibge jami’an ‘yan sanda a ƙofar shiga Gidan Gwamnantin, inda su ke aikin hana ma’aikata shiga sai mai dauke da katin shaidar riga-kafin korona.














































