Home Labaru Sauyin Sheka: Za Mu Ba Jonathan Damar Yin Takara A 2023 Idan...

Sauyin Sheka: Za Mu Ba Jonathan Damar Yin Takara A 2023 Idan Ya Dawo Cikin Mu – APC

14
0
Jonathan APC

Jam’iyyar APC, ta ce za a ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 idan ya koma cikin ta.

Sakataren kwamitin riko na jam’iyyar APC John Akpanudoedehe ya bayyana haka yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.

Ya ce komawar jonathan cikin jam’iyyar APC zai zama babban abin alfahari a gare su.

Mista John ya cigaba da cewa, za a ba Jonathan damar yin takarar kujerar shugaban kasa a shekara ta 2023, kamar kowane mutum mai sha’awar tsayawa takara.