Home Labaru Kiwon Lafiya Ciwon Koda: Fitaccen Jarumin Nollywood Amaechi Muonagor Ya Mutu

Ciwon Koda: Fitaccen Jarumin Nollywood Amaechi Muonagor Ya Mutu

46
0

Fitaccen jarumin Nollywood, Amaechi Muonagor ya mutu yana da shekara 62 a duniya, kamar yadda wani ɗan’uwansa ya shaida wa majiyarmu,

Ya mutu ne ranar Lahadi bayan ya yi fama da ciwon ƙoda da ya sa ake yi masa wankin ƙodar, in ji rahotanni daga kafafen yaɗa labarai.

Ɗan’uwan jarumin Tony Muonagor da aka fi sani da Tony Oneweek, ya tabbatar wa majiyarmu mutuwar ɗan fim ɗin ga

Mutuwar tasa na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da ya nemi tallafin kuɗi domin yi masa dashen ƙoda a Indiya.

Da yawa cikin masu son fina-finansa sun yi ta jimamin rasuwarsa a shafukan sada zumunta.

Mutuwarsa ta zo ƴan makonni bayan da Najeriya ta yi rashin wani jarumin Nollywood John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu wanda shi ma ya buƙaci tallafin kuɗi domin neman magani.

Leave a Reply