Home Labaru Cire Tallafin Man Fetur: OXFAM Ta Gargadi Najeriya

Cire Tallafin Man Fetur: OXFAM Ta Gargadi Najeriya

70
0
Kungiyar OXFAM ta gargadi gwamnatin Najeriya ta kaucewa shawarar hukumar bada lamuni ta duniya IMF wajen gaggauta kara yawan harajin VAT da cire tallafin man fetur da kuma daina banbanta yadda ake sayar da kudaden kasashen ketare.

Kungiyar OXFAM ta gargadi gwamnatin Najeriya ta kaucewa shawarar hukumar bada lamuni ta duniya IMF wajen gaggauta kara yawan harajin VAT da cire tallafin man fetur da kuma daina banbanta yadda ake sayar da kudaden kasashen ketare.

Kungiyar ta bada shawarar daukar ingantattun matakai na kusa da na nesa wadanda za su tabbatar da kara yawan kudaden da gwamnati ke kashewa domin bunkasa rayuwar jama’a maimakon dakile kudaden da hukuma ke kashewa.

Daraktan kungiyar a Najeriya Vincent Ahonsi yace kara yawan kudaden harajin VAT da kuma cire tallafin man zai dada jefa ‘Yan Najeriya da dama cikin kangin talauci.

Kungiyar OXFAM ta bayyana cewar mutane biyu da suka fi kowa kudi a Najeriya sun mallaki dukiyar da ta zarce na mutane miliyan 63 dake fafutukar samun abinda zasu ci.

Saboda wannan matsayi, kungiyar tace ya dace Najeriya ta mayar da hankali wajen karawa attajiran haraji da kuma karkata kudaden wajen gudanar da ayyukan raya kasa da suka hada da gina hanyoyi, da samar da ruwan sha da gina asibitoci da tallafawa manoma da kuma masu bincike akan yadda za’a inganta hanyar noma la’akari da yadda sauyin yanayi ke illa a duniya.

Shugaban kungiyar yace maimakon dada jefa kashi 99 na ‘Yan Najeriya cikin karin talauci, ya dace hukumomi su karbi kadan daga cikin arzikin da attajirai suka samu tun bayan barkewar annobar korona.