
Rahotannin sun nuna Jihohin Najeriya da dama sun shiga wannan makon da matsananciyar matsalar karancin man fetur, wadda daman tun bayan sati biyu da suka gabata ake cikin wannan matsala.
Rahotannin sun ce bayan kwanaki da fara fuskantar ƙarancin man sai kuma aka fara samun wani gurbataccen man fetur wanda ya rinka lalata abubuwan hawa.
A dalilin samun wannan matsala hukumomi sun bayar da umarnin dakatar da sayar da man , har ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cewa lallai sai waɗanda suka shigar da man sun yi bayani, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da kare ‘yan kasa daga duk wani abu da za a samar wanda zai cutar da su.
Wannan matsala ta karancin man dai ana ganin ta haifar da gagarumin koma-baya ga harkokin tattalin arzki na jama’a da ma gwamnati kuma za ta ci gaba da hakan har zuwa lokacin da za a shawo kanta.
You must log in to post a comment.