Home Home Hari: Saudiyya Ta Lalata Kayan Aikin Houthi a Ma’aikatar Sadarwa Ta Yemen

Hari: Saudiyya Ta Lalata Kayan Aikin Houthi a Ma’aikatar Sadarwa Ta Yemen

64
0

Rundunar ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ta ce ta kai hari kan ma’aikatar sadarwa ta Yemen da ke Sanaa babban birnin kasar tare da lalata hanyoyin sadarwa na kungiyar Houthi.

Rundunar ta ce ana amfani da ma’aikatar ne wajen kai hare-hare da jirage marasa matuƙi kan ƙasashe mambobinta.

Kawo yanzu dai babu wani bayani daga kungiyar Houthin, wadda ke samun goyon bayan Iran.