Home Home Alkalin Alkalai Ya Bukaci Majalisa Ta Rika Sa Ido Ga Bangaren Shari’a

Alkalin Alkalai Ya Bukaci Majalisa Ta Rika Sa Ido Ga Bangaren Shari’a

18
0

Alkalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad, ya yi kira ga majalisar dattawan kasar ta ja hankalinsa idan ta ga wani abu da bai dace ba yana faruwa a fannin shari’ar kasar.


Ya yi kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin
majalisar kan harkokin shari’a da kare hakkin dan adam.


ya ce “Fannin da ke yin dokoki bai ba su kunya ba kasancewar
Babu abin da suka nema suka rasa daga majalisar.


Yace akwai bukatar da zarar sunga wani abu da ba daidai ba a
fannin shari’a, su ja hankalinsu.