Home Labarai 2023: Gwamna Masari Ya Musanta Tsayawa Takarar Majalisar Dattijai

2023: Gwamna Masari Ya Musanta Tsayawa Takarar Majalisar Dattijai

11
0

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar kowane mukami na siyasa a zaben 2023.


Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa, Muntari Lawal ne ya
bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga fosta da ke
nuni da cewa gwamnan na neman takarar kujerar Sanata.


Masari ya ce bai taba tattaunawa da kowa ba kan zai tsaya takara
a kowane irin matsayi na siyasa.


Lawal ya kara da cewa idan magoya bayan Gwamnan ne suka
yada hotunan, ba su yi masa adalci ba.


Daga karshe ya bayyana hotunan a matsayin yunkuri ne kawai
na bata masa suna da kuma jam’iyyarsa APC.