Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kama Tsigaggen Shugaban Majalisar Dokoki Ta Jihar Filato

‘Yan Sanda Sun Kama Tsigaggen Shugaban Majalisar Dokoki Ta Jihar Filato

14
0

Rikicin majalisar dokoki ta jihar Filato ya dauki wani sabon salo, yayin da jami’an tsaro su ka kama tsigaggen kakakin majalisar dokoki na jihar Abok Ayuba da wasu ‘yan majalisa 10 da ke yi ma shi biyayya.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Filato Edward Ebuka, ya tasa keyar ‘yan tawagar tsohon kakakin majalisar 11 a motocin Hilux guda hudu.

‘Yan majalisar, sun ce su na nan a kan ayyukan su ga al’ummar jihar Filato, domin ganin an cimma matsaya mai ma’ana har sai an maida Shugaban Majalisar a kan mukamin sa.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Langtang ta Kudu Zingtin Sohchang, ya ce jami’an tsarosun zuba su a cikin motocin Hilux zuwa inda ba su sani ba, kuma idan bayan mintuna 20 aka kira su ba su amsa ba, to a sani cewa an kai su wurin da ba a sani ba.