Home Labaru Kasuwanci Adawa Da Sabon Tsarin Biyan Haraji: Ƴan Kasuwa Na Yajin Aiki A...

Adawa Da Sabon Tsarin Biyan Haraji: Ƴan Kasuwa Na Yajin Aiki A Uganda

46
0
Uganda fotn2019 country hero
Uganda fotn2019 country hero

Ƴan kasuwa da dama da ke Kampala a Uganda sun rufe shagunan su a ranar Talatar nan a wani ɓangare na nuna adawa da sanya tsarin haraji da ya janyo cece-kuce, kamar yadda rahotanni daga kafafen yaɗa labaran ƙasar suka bayyana.

Ƴan kasuwa da dama suna ganin sabon tsarin zai dagula harkokin su sannan kuma ya sa su biyan haraji da yawa Sun kuma ce manhajar tana da tsada sosai.

An ƙaddamar da tsarin biyan haraji na zamani ne a watan Janairun 2021 domin bibiyar ciniki da kuma harajin da ake biya, amma a baya-bayan nan ne kawai aka aiwatar da tsarin tsakanin ƙananan ƴan kasuwa lamarin da ya janyo zanga-zangar.

A makon da ya gabata, ƴan kasuwa a Kampala da sauran manyan birane sun gudanar da zanga-zangar yini biyu domin nuna adawa da tsarin biyan harajin.

Hukumar tattara haraji ta Uganda ta aiwatar da tsarin duk da damuwar da ƴan kasuwar suka nuna inda ta ce amfani da tsarin zai magance ƙin biyan haraji sannan ya sauƙaƙawa ƴan kasuwa wajen bayar da bayanan harajin su.

Leave a Reply