Home Labaru Kasuwanci A Shekara 10 A Na Cigaba Da Fuskantar Karancin Lantarki A Nijeriya...

A Shekara 10 A Na Cigaba Da Fuskantar Karancin Lantarki A Nijeriya – TCN

447
0

Nijeriya zata cigaba da fuskantar karancin wutar lantarki daga layin samar da wuta nan da shekaru goma masu zuwa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin rahotan da kamfanin samar da wutar lantarki na kasa,TCN ya gabatarwa da hukumar sanya ido a kan samar da wutar lantarki na kasa NERC.
A cewar rahoton, wannan ya faru ne sakamakon karin matsalar na’urar da ake samu da yawan samun ruwan sama da kuma karancin yawan bukata a kasar nan, wanda zai cigaba da kasancewa a kan megawatts 3,000.
Rahoton ya kara da cewa, Nijeriya zata ci gaba da fuskantar karin bukatar megawatts 15,440 da kuma megawatts 24,551 a shekara ta 2027 mai zuwa.
Binciken da hukumar kasa da kasa ta kasar Japan ta gudanar a kan TCN ya mayar da hankali ne a kan shekarar 2027 mai zuwa.

Leave a Reply