Home Labarai Tuhuma 19: Yahaya Bello Ya Fi Son A Gurfanar Da Shi A...

Tuhuma 19: Yahaya Bello Ya Fi Son A Gurfanar Da Shi A Kogi

65
0
Yahaya Bello
Yahaya Bello

Yahaya Bello, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume 19, ya aike wa babban alkalin babbar kotun tarayya,

Mai shari’a John Tsoho, yana neman a ba shi damar ya fuskanci shari’a a jihar Kogi.

Tsohon gwamnan, a cikin wasikar da ya rubuta ta hannun lauyoyin sa karkashin jagorancin Mista Abdulwahab Mohammed SAN,

ya bayyana cewa babbar kotun Lokoja ce kadai ke da hurumin sauraron tuhumar da EFCC ke masa.

Sai dai har yanzu ya kasa gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, domin ci gaba da sauraron tuhumar da ake masa,

inda lauyan ya shaida wa mai shari’a Emeka Nwite, wasikar da wanda yake karewa ya rubuta wa kotun cikin jawabin sa.

A nasa bangaren, ya bukaci kotun ta tilasta wa lauyan wanda ake kara ya bayyana dalilin da ya sa wanda yake karewa ba ya zuwa kotu,

duk da alƙawarin da ya dauka da kasancewar sa a gaban kotu, tare da kiran kotu da ta yi watsi da bukatar wanda ake karewa.

Yahaya Bello, wanda ya mulki Jihar tsawon shekara takwas, yana fuskantar tuhuma kan zargin karkatar da kuɗaɗe da almubazzaranci.

Leave a Reply