Home Labaru Zargin Bata Suna: Atiku Abubakar Ya Nemi Lauretta Onochie Ta Biya Shi...

Zargin Bata Suna: Atiku Abubakar Ya Nemi Lauretta Onochie Ta Biya Shi Diyya

504
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bukaci mai taimaka wa shugaban kasa a kan Kafafen Yada Labarai Lauretta Onochie ta roke shi afuwa, sannan ta biya shi diyya.

Wannan ya biyo bayan wani labarin da ta watsa a kafafen sadarwa na zamani, lamarin da ya sa Atiku Abubakar ya ke ganin Lauretta ta bata ma shi suna.

Babban lauyan Atiku Mike Ozekhome ya rubuta mata wasika, inda ya nemi ta karyata labarin da ta watsa, sannan ta biya Atiku diyyar naira miliyan 500 na bata ma shi suna da ta yi.

Lauyan ya kuma yi kurarin cewa, idan ba ta yi haka a cikin kwanaki biyu ba zai maka ta kotu ya kuma nemi ta biya shi diyyar naira biliyan 2.An dai rubuta wa Lauretta wasikar ne mako daya bayan ta watsa wani labari a shafin ta na Twitter, cewa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta kafa idanun ta a kan wasu al’amurra da Atiku ke yi a kasar da su ka jibinci mu’amala da ‘yan ta’adda.

Leave a Reply