Home Labaru Zargi: ‘Yan Siyasa Da Boko Haram Na Shirin Tarwatsa Jihar Zamfara –...

Zargi: ‘Yan Siyasa Da Boko Haram Na Shirin Tarwatsa Jihar Zamfara – Gwamna

227
0
Bello Muhammad Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara
Bello Muhammad Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara, ta ce ta samu rahotannin sirri game da kulle-kullen da wasu ‘yan siyasa ke yi domin su tarwatsa Jihar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Zamfara Yusuf Gusau ya fitar, ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa su na kulle-kulle tare da hadin baki da Boko Haram don a rika kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba hare-hare.

Jami’in ya kara da cewa, shirin da marasa kishin ke yi shi ne, su lalata sulhun zaman lafiyar da aka cimmawa tsakanin gwamnati da ‘yanbida  a jihar Zamfara.

Ya ce masu wannan mugun nufin sun yi shirin kai hare-hare a kananan hukumomi bakwai na jihar, da kuma wasu muhimman wurare da ke cikin birnin Gusau.

Ya ce Kananan hukumomin da aka shirya kai wa hare-haren sun hada da Gusau da Tsafe da Talata Mafara da Anka da Zurmi da Maru da kuma Maradun.