Gwamnatin Jihar Zamfara, ta ce ta samu rahotannin sirri game da kulle-kullen da wasu ‘yan siyasa ke yi domin su tarwatsa Jihar.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Zamfara Yusuf Gusau ya fitar, ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa su na kulle-kulle tare da hadin baki da Boko Haram don a rika kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba hare-hare.
Jami’in ya kara da cewa, shirin da marasa kishin ke yi shi ne, su lalata sulhun zaman lafiyar da aka cimmawa tsakanin gwamnati da ‘yanbida a jihar Zamfara.
Ya ce masu wannan mugun nufin sun yi shirin kai hare-hare a kananan hukumomi bakwai na jihar, da kuma wasu muhimman wurare da ke cikin birnin Gusau.
Ya ce Kananan hukumomin da aka shirya kai wa hare-haren sun hada da Gusau da Tsafe da Talata Mafara da Anka da Zurmi da Maru da kuma Maradun.














































