Home Labaru Ku Rika Kasancewa Da Katin Shaida – Rundunar Soji Ga Mazauna Arewa...

Ku Rika Kasancewa Da Katin Shaida – Rundunar Soji Ga Mazauna Arewa Maso Gabas

193
0

Dakarun Operation Lafiya Dole na rundunar sojin Nijeriya da ke Maiduguri, ta ce sun soma gudanar da aikin tantance ‘yan Boko Haram da mayakan kungiyar ISWAP da ke buya a wasu kauyukan jihohin Borno da Yobe.

Ta ce an bukaci mazauna da al’umman yankin arewa maso gabashin Nijeriya, su rika kasancewa dauke da katin shaida mai inganci a jihohin Adamawa da Borno da Yobe. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakakin rundunar Kanar Ado, ya ce an umurci dakarun rundunar su gudanar da bincike da kuma duba ingantaccen katin shaidar al’umman yankin, sannan ya ya lissafa hanyoyin da za a tantance mutane, wandanda su ka hada da katin shaidar zama dan kasa da katin zabe da lasisin tuki da kuma Fasfo.