Home Labaru Kididdiga: Hare-Haren ‘Yan Bindiga Ya Fi Na Boko Haram Barna A Nijeriya...

Kididdiga: Hare-Haren ‘Yan Bindiga Ya Fi Na Boko Haram Barna A Nijeriya – Rahoto

255
0

Wata kididdiga da kafafen yada labarai na Nijeriya su ka gudanar, ta nuna cewa hare-haren ‘yan bindiga sun kashe mutane sama da yadda kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin tsageru suka yi a cikin watanni 9 da su ka gabata.

Kungiyar Boko Haram, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar dubban ‘yan Nijeriya a shekaru 10 da su ka gabata, ta kasance a kan gaba cikin kungiyoyi masu ta’asa da salwantar da rayuka kafin yanzu.

Nazarin da jaridu suka yi daga watan Janairu zuwa Satumba ya nuna cewa, ‘yan bindiga da ke gudanar da ta’asar su a arewacin Nijeriya sun ture Boko Haram zuwa matsayi na biyu a wadanda ke yi wa ‘yan Nijeriya kisan mummuke.

Yayin da Boko Haram ta kashe mutane 370, wato kusan kashi 19 na ‘yan Nijeriya 1,950 da kungiyoyi masu aika-aika su ka kashe, ‘yan bindiga sun kashe mutanen da su ka ninka haka, inda su ka kashe 875, kusan kashi 45 na adadin mutanen da su ka salwanta.

Kungiyoyin asiri da ‘yan fashi da makami da masu satar mutane da sauran su kuwa, sun kashe mutane 705 a sassan Nijeriya, wato kashi 36 na adadin kenan.