Home Labaru Zamfara: Al’ummar Kauyuka 6 Sun Fara Komawa Gida – Mutawalle

Zamfara: Al’ummar Kauyuka 6 Sun Fara Komawa Gida – Mutawalle

740
0
Bello Muhammed Mutawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammed Mutawalle, ya bukaci mazauna jihar su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin dorewar zaman lafiya.

Gwamnan Mutawalle, ya bayyana hakan ne a lokacin da  mazauna garuruwan shida da suka hada da Lilo, Fura Girke, Kowha, Kundumau,Yargeba da Bundugel sun koma gidajensu, bayan ci gaba da aka samu kan tsaro a jihar.

Mai  ba gwamnan jihar Zamafara shawara akan harkokin tsaro, Abubakar Muhammad Dauran, ya ce wasu daga cikinsu sun shafe tsawon watanni shida a yankin Mada dake karamar hukumar Gusau, amma sun samu komawa gidajensu bayan matakin da gwamnatin jihar a karkashi jagorancin Gwamna Bello Mutawalle ta dauka.

Gwamna Matawalle ya yaba wa kokarin gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta ba jihar Zamfara kulawa ta musamman ta hanyar tura karin jami’an tsaro wanda ya yi sanadiyyar dawowar zaman lafiya a jihar.Gwamnan ya kuma bukaci manoma a jihar su koma bakin aikin su bayan an dauki matakan da suka dace domin tabbatar da ba su kariya da dukiyoyin su.

Leave a Reply