Home Labaru Rikicin Majalisar Bauchi: Oshiomole Ya Gargadin Gwamnan Jihar

Rikicin Majalisar Bauchi: Oshiomole Ya Gargadin Gwamnan Jihar

678
0

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa Adams Oshiomole ya yi kira ga gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad ya bari a bi doka da oda wajen zaben kakakin majalisar Bauchi.

Oshiomole,  ya ce babu yadda za ayi PDP ta fitar da kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisa a majalisar ta jihar Bauchi.

Oshiomole ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da yan majalisar jihar Bauchi na jam’iyyar APC, inda ya shawarci  gwamnan Bauchi ya bi doka da oda wajen tabbatar da cewa jam’iyya mai rinjaye ta fitar da kakakin majalisa da mataimakin kakkaki da sauran shugabannin majalisar dokoki.

Oshiomole ya ce tun da APC ba ta yi amfani da karfin mulki ba ta murde wa gwamnan nasarar sa, shi ma kada ya yi amfani da jami’an yan sanda, wajen hana wa yan majalisar jihar na jam’iyyar APC yancin su.

Leave a Reply