Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammed Mutawalle, ya bukaci mazauna jihar su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin dorewar zaman lafiya.
Gwamnan Mutawalle, ya bayyana hakan ne a lokacin da mazauna garuruwan shida da suka hada da Lilo, Fura Girke, Kowha, Kundumau,Yargeba da Bundugel sun koma gidajensu, bayan ci gaba da aka samu kan tsaro a jihar.
Mai ba gwamnan jihar Zamafara shawara akan harkokin tsaro, Abubakar Muhammad Dauran, ya ce wasu daga cikinsu sun shafe tsawon watanni shida a yankin Mada dake karamar hukumar Gusau, amma sun samu komawa gidajensu bayan matakin da gwamnatin jihar a karkashi jagorancin Gwamna Bello Mutawalle ta dauka.
Gwamna Matawalle ya yaba wa kokarin gwamnatin tarayya a karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta ba jihar Zamfara kulawa ta musamman ta hanyar tura karin jami’an tsaro wanda ya yi sanadiyyar dawowar zaman lafiya a jihar. Gwamnan ya kuma bukaci manoma a jihar su koma bakin aikin su bayan an dauki matakan da suka dace domin tabbatar da ba su kariya da dukiyoyin su.