Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Sojin Najeriya Ta Fito Da Sabon Salo

Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Sojin Najeriya Ta Fito Da Sabon Salo

897
0

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta fitar da sabbin hanyoyin murkushe ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ciki hadda na’urar daukan hotunan sirri.

Babban kwamandan rundunar sojin kasa ta 8 dake kula da jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Katsina Birigediya Janar Abdulkarim Oladapo Okiti ne, ya bayyana haka a yayin da ya kai wa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ziyara.

Kwamandan ya ce ziyarar nada nasaba da umarnin shugaban kasa kan cewa dole ne a tashi tsaye domin ganin sun murkushe ayyukan ‘yan bindiga a  yankin.

Ya ce akwai wasu tsare-tsare na daban da suka sauya domin kawo karshen ta’addancin ‘yan bindiga,  bugu da kari, ya ce yin amfani da zamani ya zama wajibi saboda badda-kama ga ‘yan ta’adda.

Leave a Reply