Hukumar yaki da rashawa atyyukan zamba ICPC, ta ce an daure tsohon Shugaban Hukumar Gudanarwa na Babbar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kwara Alanamu a gidan yari saboda laifin rashawa.
An dai daure Alanamu ne, tare da babban daraktan kamfanin Namylas Nig. Ltd Salman Sulaiman, saboda laifin karba da kuma bada cin hanci.
Tun farko an gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Abdul-Gaffar na Babbar Kotun Jihar Kwara da ke Ilorin, bisa tuhume-tuhume takwas da su ka kunshi karba da kuma bada rashawa.
An dai kama Alanamu ne da laifin karbar cin hancin naira miliyan 5 daga wani abokin sa dan kwangila a matsayin kashe-mu-raba, yayin da aka zargi Salman Sulaiman da laifin bada cin hanci ga jami’in gwamnati, ta hanyar zuba kudaden a asusun Alanamu na Bankin GT.
Tuni dai kotu ta yanke wa Alanamu hukuncin biyan naira miliyan 25 tare da zaman shekaru biyar a gidan yari, yayin da aka daure Sulaiman shekaru bakwai a gidan yari da biyan tarar naira miliyan daya.