Sanata Ali Ndume wanda ɗan majalisar ƙungiyar ECOWAS ɗin ne ya bayyana haka a Kano,
a yayin da majalisar ƙungiyar ke ci gaba da gudanar da taron ta a jihar.
Dan majalisar ya ce an cimma duk wani abu da ake buƙata domin maido da ƙasashen cikin ƙungiyar ta Ecowas.
Ya ce an riga an warware saɓanin da ya kai ga ɗaukar matakin fita daga ƙungiyar,
kuma a yanzu duka ƙasashen sun huce daga fushin da suke yi da ECOWAS,
saboda haka ga dukkan alamu a shirye su ke su dawo cikin ƙungiyar.
Ƙasashen uku dai sun ɗauki matakin fita daga ƙungiyar ne bayan da ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen, tare da sanya musu jerin takunkumi.














































