Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Buratai Ya Kara Tabbatar Da Murkushe Boko Haram

Yaki Da Ta’addanci: Buratai Ya Kara Tabbatar Da Murkushe Boko Haram

409
0

Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya Tukur Buratai, ya kara jaddada cewa, tuni sojoji sun murkushe Boko Haram ta hanyar kakkabe su baki daya.

Janar Buratai ya ce, wadanda ake yaki da su a yanzu gungun rikakkun manyan Boko Haram na kungiyar ISWAP ne, masu ganin sai sun kafa shari’ar musulunci a Afrika ta yamma.

Ya ce abin da ke faruwa a Arewa maso gabashin Nijeriya a yanzu, maharan kungiyar ISWAP ne da su ka zama rikakkun mabarnata a duniya, su ka yi ambaliya su na karya doka tare da kai hare-hare a yankin Afrika ta Yamma.

Janar Buratai ya bayyana haka ne, yayin da wasu dalibai su ka kai masa ziyara, don su koyi darasi daga wani littafi da aka buga a kan tarihin shi mai suna ‘The Legend of Buratai’.

Leave a Reply