Home Labarai Har Yanzun Babu Labarin Fasinjojin Da Yan Bindiga Suka Sace

Har Yanzun Babu Labarin Fasinjojin Da Yan Bindiga Suka Sace

4
0
43723b427bcc2b2392cf259309420c86
43723b427bcc2b2392cf259309420c86

Jami’an sun ce har yanzu ba su sami wani bayani game da fasinjojin da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.

Tun makon jiya ne dai ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wadannan fasinjoji da suka fito daga jihar Edo zuwa Abuja.

Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa, ta na kan bincike akan lamarin.

Kwamishinan Labarai na jihar Kogin ya ce suna hada hannu da Jami’an tsaro domin gano abinda ya faru da kuma kokarin kubutar da fasinjojin.

Ya ce, sun kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro a nan jihar Kogi kuma sun samu jerin sunayen fasinjojin

amma ana kan bincike har ya zuwa yanzu domin tabbatar da an kubutar dasu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar kogi Mr.William Aya,

 ya ce, har ya zuwa ranar litanin din nan babu wani ci gaba da suka samu akan lamarin amma dai suna kan bincike.

Leave a Reply