Home Labaru Kasuwanci Ibtila’in Gobara: Kasuwar Karu A Abuja Ta Kone Kurmus

Ibtila’in Gobara: Kasuwar Karu A Abuja Ta Kone Kurmus

25
0
Market Fire 3
Market Fire 3

Wata mummunar gobarar da ta auku a kasuwar Karu da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

kasuwa dai tana kusa da mahadar Abuja da jihar Nasarawa, kuma ana samun masu zuwa cin kasuwar daga Abuja kullum.

Ya zuwa yanzu kasuwar ta kone kurmus da dukkan kayayyakin da ke cikin ta,wanda ba’a iya kayyade kudin su ba,

inda ‘yan kasuwar da suka tafka asara suka shiga cikin halin dimuwa da kaduwa sosai.

Hukumar Kashe Gobara a kasuwar ta fitar da sanarwa cewa ta fuskanci kalubale wajen isa cikin kasuwar,

domin babu hanya saboda cunkoson kayayyaki, shi ya sa ba ta iya kashe wutar da wuri ba.

 Hukumar kashe gobara ta ce Gobarar ta fara ne da misalin karfe 7 na yammacin jiya,

bayan mutane da dama sun rufe shagunan su, wasu kuma suna kokarin fita daga kasuwar.

Ta ce ba’a san musabbabin tashi wutar ba amma tana ganin kamar tangardar lantarki ne ya jawo gobarar,

sai dai ba’a rasa rayuka ba, amma an samu lalacewar kayayyaki da aka kiyasta sun kai na miliyoyin Naira.

Leave a Reply