Mun samu labarin rasuwar tsohuwar jarumar Kannywood, Fati
Slow.
Wannan na cikin wani sako da tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa, Mansura Isah ta wallafa ne a shafinta na Instagram
Mansura ta ce tsohuwar jarumar ta rasu ne a wani gari Abasha da ke kusa da Sudan, kuma tuni aka yi jana’izar ta a can.
A cewar ta yanzu haka ana zaman makokin ta a gidan su da ke Unguwa Uku a Jihar Kano.














































