Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa, shugaba Bola Tinubu ya samu nasarar samawa Najeriya jarin sama da dala biliyan 20.
Shettima ya ce wadannan jarin sun hada da dala biliyan 14 daga kasar Indiya da kuma dala miliyan 250 daga kasar Netherland, tare da alkawurran dala miliyan 500 kowannen su na bunkasa ma’adanai a jihar Nasarawa da kuma daga kasar Jamus.
Shettima ya bayyana haka ne a taron tattalin arziki da aka gudanar a Legas mai taken, “Sauye-sauye a Zamanin Tattalin Arziki na Duniya”.
Shattima wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Tope Fasua, ya bayyana cewa kokarin na daya daga cikin dabarun gwamnati na tunkarar kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta.
Ya jaddada mahimmancin ci gaban fasaha da dabarun gudanar da sauye-sauye yadda ya kamata, yana mai bayyana cewa akwai goyon baya na ayyukan bangaren samar da wutar lantarki na kamfanin Siemens da nufin bunkasa wadatar makamashi.














































